Cikin wata sanarwa da ofishin na tawagar UNMISS ya fitar a birnin Juba, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa tabbas sansanin aka hara kai tsaye, duba da cewa sansanin sananne ne, kuma babu wasu dakaru dake kusa da wurin lokacin da aka kaddamar da harin.
Bisa hakan, ofishin MDD ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a Sudan ta Kudu da su kiyaye alfarmar jami'an tsaron MDD, da kayayyakin aikin su, da kuma matsugunnan fararen hula.
Harin dai ya auku ne kwana guda, gabanin isar shugaban 'yan tawayen kasar Riek Machar birnin Juba, wanda ya amshi mukamin mataimakin shugaban kasar, kamar yadda shirin wanzar da zaman lafiya na watan Agustar bara ya tanada.
Masu aikin jin kai dai na nuna kyakkyawan fatan komawar Mr. Machar gwamnatin kasar, zai iya wanzar da shirin dakatar da bude wuta, tare da baza damar shigar da kayan agaji ga wadanda ke matukar bukatar hakan.
Yakin basasa ya barke a kasar ne cikin watan Disambar shekarar 2013, lokacin da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi mataimakin sa Mr. Machar da yunkurin kifar da gwamnatin sa, zargin da Machar din ya sha musantawa. (Saminu Alhassan)