Mai rikon mukamin ministan harkokin wajen kasar Bashir Gbandi, ya fadawa 'yan jaridu a Juba cewar, gwamnati ta amincewa Machar ya koma kasar tare da rakiyar rundunar mayaka 195 da kuma babban dogarinsa.
Shi dai Machar zai koma Juba ne domin kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da shugaban kasar Salva Kiir, sai dai a sau biyu ana katse hanzarin komawar tasa saboda bukatar da ya nema na shiga Juba da dakaru masu yawa da manyan makamai a cikin wannan mako.
Ana saran za'a rantsar da Machar da zarar ya koma, kuma ya bukaci babban jami'in rundunar mayakan gwagwarmayar kwatar yanci ta SPLA-IO Simon Gatwech Dual wanda ke karkashin binciken Amurka da MDD daya fara isa Juba don jagotantar tawagar soji da 'yan sanda na su kimanin 1,370,wadanda suka riga suka isa Juba.
Gbandi, yace gwamnati ta biya dukkan kudaden jiragen da zasu tashi zuwa Juba, kimanin jirage 3 da aka dauki hayarsu, sai dai bayan da jakadan Amurka ya tuntubi Machar yace babu tabbas ko jiragen zasu tashi a wannan rana, amma ana ta kokarin tabbatar da yiwuwar hakan.
An sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ne a watan Augasta, domin kawo karshen yakin basasar kasar da ya shafe shekaru biyu, inda aka amince Machar zai koma kujerarsa ta mataimakin shugaban kasar yayin da Kiir zai cigaba da zama shugaban kasa.
Gbandi ya yabawa kasashen Amurka da Birtaniya da Norway da kasar Sin, bisa taimakon da suka bayar domin samo bakin warware rikincin kasar.
Fada ya barke ne a jaririyar kasar tun bayan samun 'yanci daga kasar Sudan a shekarar 2011, tsakanin Machar da shugaban kasar Salva Kiir, wanda ya zargi mataimakinsa Machar da yunkurin juyin mulkin don kifar da gwamnatinsa, zarginda mista Machar din ya sha musantawa.
Rikicin yayi sanadiyyar hasarar dubban rayukan jama'a, sannan sama da mutane miliyan 2 suka tsere daga matsugunan su.(Ahmad Fagam)