Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da takwaransa na Tanzaniya John Magufuli, shugaba mai ci na kungiyar EAC, sun rattaba hannu kan kundin shigar ta Juba cikin wannan gungun na shiyyar.
Da yake magana bayan bikin rattaba hannu, shugaba Magufuli ya jinjinawa Sudan ta Kudu, tare da bayyana cewa bikin wani abun tarihi ne, da kuma ke fadada kasuwar shiyyar dake da mutane kusan miliyan 160.
Domin ganin EAC ta samu cigaba mai karko, dole ne a fifita zaman lafiya, in ji shugaba Magufuli, tare da yin kira da sabon zuwan cewa da shugaba Salva Kiir da ya cigaba da yin shawarwarin domin tabbatar da kawo karshen yake yake a cikin wannan kasa.
A nasa bangare shugaba Kiir ya bayyana jin dadinsa da yadda shugabannin EAC suka amince da shigowar kasarsa cikin wannan kungiya ta shiyya, kungiyar da ake girmamawa a duniya, tare da bayyana cewa Sudan ta Kudu ta zo gida ne.
Ministan harkokin wajen Tanzaniya Augustine Mahiga, ya bayyana cewa EAC za ta aiki yadda ya kamata tare da gamayyar kasa da kasa domin tabbatar da dawowar 'yan Sudan ta Kudu da suka tsere daga kasarsu a lokacin tashe tashen hankalin siyasa. (Maman Ada)