A watan Febrairu na bana, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bayar da sanarwa, inda ya yi kira ga Machar da ya koma birnin Juba cikin hanzari, don shiga shirin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar don cimma yarjejeniyar warware rikicin kasar Sudan ta Kudun tsakanin bangarorin biyu kamar yadda suka daddale a shekarar bara.
Machar ya bayyana a kwanakin baya cewa, idan dakarunsa sun koma birnin Juba, zai tashi zuwa birnin Juba don shiga shirin kafa gwamnatin wucin gadi a ranar 18 ga wannan wata. (Zainab)