in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan kwagilan Senegal: An bukaci kafofin Sin da na Afrika su yi aiki tare domin bunkasa makomar dangantaka Sin da Afrika
2016-05-01 12:44:32 cri
Wani hamshakin dan kwagila na Senegal Sourakhata Tireka, dake zama a nan Sin, yayi kira a ranar Asabar ga kafofin watsa labarun Sin da na Afrika da su yi aiki tare domin bunkasa makomar dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika, a yayin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Dan kasar Senegal din yana zama a Yiwu dake gabashin Sin tun a shekarar 2004, inda ya kafa wani kamfaninsa, Crestone Group, kana kuma wanda ya kirkiro dandali na farko na zuba jari masu zaman kansu na kasar Sin a birnin Dakar.

Ya nuna cewa idan Sinawa sun samu bayanai masu kyau kan Afrika, ba za su ji tsoron zuba jari a Afrika ba.

Dole ne kafofin watsa labarai su wayar da kai da watsa al'adu, da hakikanin gaskiya game da Afrika da kuma Sin. Wannan shi ne muhimmin mataki, domin idan yanzu Sinawa sun samu bayanan da ya dace ta hanyar kafofin watsa labarai kan Afrika, to ko shakka babu ba za su damu game da zuwa zuba jari a Afrika ba, in ji mitsa Tirera.

Tirera yana kira ga dukkan kafofin sadarwa na Sin da Afrika da su yi aiki tare cikin hadin gwiwa domin bunkasa makomar dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika.

A cewar wannan dan kasuwa, dole ne 'yan kasar Senegal su rike wadannan damammaki da dangantakar Sin da Afrika ke samarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China