A cikin kudurin, kwamitin sulhun ya tsaida tsawaita wa'adin rukunin masana na kwamitin sakawa Sudan ta Kudu takunkumi zuwa ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2016. Kana sanarwar shugaba ta yi maraba da bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su aiwatar da yarjejeniyar warware rikicin kasar Sudan ta Kudu, ciki har da tabbatar da tsaro a Juba yadda ya kamata, kana sanarwar ta kalubalanci bangarorin da su ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da nuna goyon baya ga jama'ar kasar. (Zainab)