Mutane na ci gaba da shiga kasashe makwabta, amma cikin karamin adadi a 'yan makwannin baya bayan nan, a yayin da abubuwa suke matukar wahala na ratsa kan iyakoki. Mutane da dama dake neman hijira da sabbin zuwa na bayyana cin zarafin dan Adam da ake ci gaba da yi a kasar Burundi, da suka hada azabtarwa, fyade, tsare mutane ba bisa doka ba, takurawa, tilastawa mutane shiga kungiyoyin sa kai, kisan kai da makamantan haka, in ji kakakin HCR, a cikin sanarwar MDD.
A cewar HCR, ci gaban tallafin kasa da kasa na da muhimmanci sosai wajen rage zaman dar dar da kuma taimakawa yin shawarwarin tsakanin bangarori masu gaba da juna na kasar ta Burundi. (Maman Ada)