Ministan tsaron kasar Burundi Emmanuel Ntahomvukiye ya fidda sanarwa da ke cewa da karfe 7 na safiyar jiyan ne aka kaddamar da hari kan motar da Kararuza ke ciki, inda nan take Kararuza da matarsa, tare da daya daga masu gadin sa suka rasa rayukan su, kana wata 'yar sa, da direban sa, da wani mai gadin daban suka ji rauni. Sanarwar ta yi Allah wadai da wannan hari.
Rahotanni na cewa, Karazuza shi ne babban jami'i cikin manyan hafsoshi biyar da aka kaiwa hari aka kuma hallaka su a birnin Bujumbura fadar mulkin kasar cikin makwannin da suka gabata.
Tun daga watan Afrilu na shekarar 2015, ake samun tashe-tashen hankula a kasar Burundi, inda aka kaddamar da hare-hare da dama a kasar. An ce tashe-tashen hankula dake karuwa a kasar sun haddasa mutuwar mutane fiye da 400, kana mutane fiye da dubu 200 sun tsere zuwa sauran kasashen dake makwabtaka da Burundin. (Zainab)