Wannan yana nuna cewa, Yoweri Museveni zai fara wani sabon wa'adin shugabancin kasa na tsawon shekaru biyar, bayan shafe shekaru 30 yana rike mulkin kasar ta Uganda.
'Yan yan takara 8 ne suka fafata a zaben na bana. Ban da Yoweri Museveni, dan takarar jam'iyyar NRM dake rike da mulkin kasar, sai kuma dan takarar jam'iyyar adawa mafi girma ta FDC mista Kizza Besigye wanda sau hudu ke nan yana tsayawa takarat zaben shugaban kasar. A wannan karo ya sami kashi 35.37 cikin 100 na kuri'in da aka kada. Dan takara mai zaman kansa, kana tsohon firaministan kasar, Amama Mbabazi ya sami kuri'u kashi 1.43 cikin dari, wanda ya zo na uku. Bayan da aka bayyana sakamakon babban zaben, dan takarar jam'iyyar adawa, Kizza Besigye ya ba da sanarwar cewa, an tafka magudi a zaben, don haka ya yi kira da sake kidaya kuri'un. (Fatima)