in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Santos na neman Euro miliyan 10 domin sayar da Zeca ga Atletico Madrid
2016-04-27 17:02:37 cri
Kungiyar kwallon kafar Santos ta Brazil, na bukatar Euro miliyan 10 daga kungiyar Atletico Madrid, kafin amincewa ta sayar da dan wasan ta José Carlos Cracco Neto, wanda aka fi sani da Zeca.

A cewar kafar watsa labarun wasanni ta Samba foot, dan wasan mai shekaru 21 da haihuwa, ya ja hankalin kungiyar ta Atletico Madrid bisa kwarewar da yake nunawa a kungiyar ta sa wato Santos a wannan shekara.

Kaza lika kafar ta ce kungiyar ta yi watsi da bukatar sayen dan wasan daga wani kulaf din Sifaniya na daban, bayan da kulaf din ya taya Zeca kan kudi Euro 8.

Shi dai kulaf din Atletico Madrid na fatan kammala sayen Zeca, kafin gudanar gasar Olympics dake tafe nan da 'yan watanni, duba da cewa bayan gasar ta Olympics, farashin dan wasan na iya hauhawa. Zeca dai ya fara bugawa kungiyar Santos tamaula ne cikin shekarar 2014, bayan da ya samu ci gaba daga kulaf din horaswa na kungiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China