in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bada sharadi game da daukar hayar mai horas da yan wasa daga ketare
2016-04-06 16:18:47 cri

Gwamnatin Najeriya ta baiwa hukumar gudanarwar kwallon kafa ta kasar sharruda game da dauko hayar mai horas da 'yan wasa a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar.

Ministan harkokin matasa da wasanni na Najeriyar Solomon Dalung, ya tabbatar da hakan, inda ya bukaci kwamitin tsare tsare na hukamar wasannin kasar, ya gabar masa da kwararan hujjojin da zasu gamsar dashi game da kwarewar da mai horas da yan wasan da za'a dauko hayar tasa yake dashi.

Dalong ya shedawa yan jaridu cewar, batun dauko hayar kociya daga kasar waje abu ne dake bukatar yin zazzafar mahawara kansa, amma duk da hakan za'a damka alhaki ga hannun kwamitin kwararru na hukumar ta NFF domin sanin kudaden da za'a kashe da kuma dalilan da zasu sanya dauko hayar kociyan daga ketare.

Ya kara da cewar kuskure ne mutane su dinga yin kiraye kiraye na neman shugaban hukumar NFF na kasar Amaju Pinnick ya yi murabu, kasancewar kasar ba zata samu zarafin shiga gasar wasannin na kofin kasashen African a shekarar 2017 ba.

Dalung yace rashin kwanciyar hankali game da daukar hayar mai horas da yan wasan kasar, da gutsuri tsoma, da rashin isassun kudade ne suka hana kulub din na Super Eagles samun nasarar tsallake rijiya da baya a wasannin share fagen.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China