in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kanu ya yi hasashen makoma mai haske ga Alex Iwobi na Arsenal
2016-04-06 16:16:56 cri
Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafar Najeriya Nwankwo Kanu, ya ce matashin dan wasan kungiyar Super Eagles wanda ke bugawa Arsenal kwallo Alex Iwobi, na iya kasance fitaccen dan wasa a gasar Firimiyan kasar Ingila.

Iwobi, dan shekaru 19 ya ci kwallon sa ta biyu a gasar firimiya ta bana ga kungiyar ta Arsenal, a wasan da suka samu nasarar doke Watford da ci 4 da nema. A cewar Kanu, Iwobi na da basira da saukin kai, yana kuma daukar shawara, da ganin takun sa kuma zai taka rawar gani yadda ya kamata.

Kanu wanda ya bugawa Arsenal wasa a kakar wasanni biyu, a nasa lokaci ya ci wa kungiyar kwallaye 30 a wasannin 119 da ya buga.

Iwobi dai dan uwa ne ga Jay Jay Okocha, wanda shi ma ya takawa Najeriya kwallo a baya, ya kuma shiga jerin 'yan wasan Super Eagle a karon farko, a zagaye na daya na wasan share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka na hukumar AFCON wanda za a buga a badi, wanda Najeriyar ta bugu da Masar, aka kuma tashi 1-1 kafin daga bisani Masar din ta fidda Najeriya a zagaye na biyu na wasan da suka buga a birnin Alkahira.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China