in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar zai buga wasa a Copa na Amurka da gasar Olympics
2016-04-06 16:12:28 cri
Neymar zai iya buga wasa a gasar Copa Amurka da kuma gasar Olympic a kakar wasanni ta wannan karo, duk da rashin gwarin gwiwar da kulub dinsa na Barcelona ya nuna kan wannan batu.

Shugaban Barcelona Jose Bartomeu, ya fada a ranar Asabar cewa, ba zai yiwu Neymar ya tauna taura biyu a lokaci guda ba.

To sai dai wani jami'in wasanni na ksar Brazil Wagner Ribeiro, ya ce, dan wasan mai shekaru 24 a duniya, bai fidda rai ba wajen gamsar da Barcelona game da kudirinsa na taka leda a wasannin biyu.

Ribeiro, ya ce Neymar yana da burin buga wasannin biyu, kamar yadda aka rawaito shi ya ambata a jaridar Globo newspaper, ya ce sun yi kokarin cimma daidaito da Barcelona, don bashi dama ya zaba cikin wasannin biyu. Amma tuni Neymar, ya yanke kudiri a zuciyar sa na buga wasannin biyu.

Ita dai gasar Copa America za a buga ta a Amurka tsakanin 3 zuwa 26 ga watan Yuni, yayin da a daya bangaren, za'a gudanar da wasannin Olympic a birane 6 na kasar Brazil tsakanin 3 zuwa 20 ga watan Augusta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China