in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benzema ya yi watsi da zargin da ya sabbaba dakatar da shi daga tawagar kungiyar kasar Faransa
2016-03-16 16:36:25 cri
Dan wasan gaban kungiyar Real Madrid Karim Benzema, ya maida martani ga zargin da aka yi masa na cin zarafin wani dan wasan kwallon mai suna Mathieu Valbuena, ta hanyar fidda wani faifan bidiyo na badala dake da alaka da Valbuena wanda ke wasa a Lyon na kasar ta Faransa.

A farkon makon nan ne dai Firaministan kasar Faransa Manuel Valls, ya soki dan wasan da nuna rashin da'a, yana mai cewa kwallon kafa ta wuce batun 'yan kallo, harka ce dake bukatar mutane da zasu zamo kyakkyawan misali ga sauran al'ummar Faransa.

Firaminstan Valls ya kara da cewa duk da yake ba shi ne shugaban hukumar kwallon kafar Faransa ba, amma a ganin sa bai dace a baiwa Benzema damar shiga tawagar kwallon kasar ba.

Shi ma ministan wasannin Faransa Patrick Kanner, ya goyi bayan wannan ra'ayi na Mr. Valls, inda ya ce Benzema bai cika sharuddan sake komawa tawagar kasar ba, tun da dai kotu na ci gaba da binciken zargin da ake yi masa, ya kuma nuna shakku ga matsayin da'ar dan wasan, da biyayyar sa ga dabi'un al'ummar kasar ta Faransa

Da fari dai an zare sunayen Benzema da Valbuena daga jerin 'yan wasan Faransa, kafin wasu rahotannin baya bayan nan su nuna cewa Benzema ya tsallake takunkumin dakatarwar da aka yi masa, inda yanzu haka yake da damar komawa kungiyar ta Faransa da kwallo.

A wani sako da ya aike ta shafin sa na Twitter, Benzema ya nuna yadda ya buga wasanni 541, ba jan kati ko daya, yalon kati 11, don haka a cewar sa bai ga dalilin da zai sanya ace shi ba abun misali ba ne. An ce Benzema na iya fuskantar daurin shekaru har 5, idan har aka tabbatar da zargin da ake yi masa na cin zarafin Valbuena.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China