in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon kociyan Najeriya ya janye karar da ya shigar NFF
2016-03-16 14:42:12 cri

Tsohon mai horas da yan wasan kulub din Super Eagles na Najeriya Sunday Oliseh, a ranar Talatar da ta gabata ya umarci lauyansa da ya janye karar daya shigar hukumar wasan kwallon kafa ta kasar NFF.

Tsohon kociyan ya ce, ya dauki wannan mataki ne bayan da wasu mutane masu kima a kasar suka shawarce shi da ya aiwatar da hakan.

Oliseh ya bayyana hakan ne a shafinsa na Youtube wanda shi ne ya yi amfani wajen bayyana yin murabus daga shugabancin hukumar, a makwani biyu da suka gabata.

Shi dai mista Oliseh, ya nuna cewar, daya cikin dalilan da suka sanya ya kauracewa jagorancin NFF har da rashin biyansa kudaden albashi.

A farkon wannan wata ne yayi barazanar maka hukumar kwallon kafar Najeriyar a kotu, sai dai hukumar kwallon kafa ta kasar ta tabbar da cewar duk wasu hakkokinsa da yake kuzuzuta yana bin hukumar an riga da an biya shi tun gabannin yayi murabus.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China