Cimma karfin wutar lantarki zai taimakawa Burundi, tabbatar da ganin cewa dukkan bangarorin al'ummar kasar sun samu farashin wutar lantarki mafi sassauci, tare da baiwa kowa damar samun makamashi na zamani.
A halin yanzu, kasar Burundi na amfani kawai da megawatt 66.35, kuma asarar da ake samu ta kusan MW 30 zuwa 35 nada nasaba da tsufan gine ginen kamfanin samar da ruwa da wutar lantarki na REGIDESO da aka kafa tun a shekarar 1960. (Maman Ada)