Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana hakan a Juma'ar da ta gabata.
Mista Liu ya ce, burin kasar Sin game da wannan batu shi ne, tana karfafa gwiwa ga kasashen nahiyar Afrika da su tashi tsaye wajen gayyato dukkanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna, don zama a teburin sulhu domin warware rikicin kasar.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta bayyana matsayinta game da rikicin Burundin da cewar, tattaunawar sulhu ce kadai za ta kawo karshen dambarwar siyasar kasar ta Burundi, kuma wannan kudurin ya samu amincewar wakilai 15 na kwamnitin MDD.
MDD ta nemi kasashen dake yankin da su bada gudumawa don warware rikicin siyasar da yaki ci yaki cinyewa a kasar Burundin, kuma a dauki dukkan matakan dakile ayyukan 'yan tawaye masu dauke da makamai. (Ahmad Fagam)