Mista Machar yayi wannan sanarwa a cikin wata wasikar da ya mika a ranar Laraba ga kwamitin hadin gwiwa na sanya ido da kimantawa (JMEC), wata hukumar dake kula ga sanya ido ga aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
A cewar mista Machar, ya tabbatar da zuwasa birnin Juba a ranar 18 ga watan Afrilu, bayan wannan za a kafa gwamnatin wucin gadi tare da shugaba Kiir da kuma halatar taron ministocin kasa na wucin gadi. (Maman Ada)