Kanar Baratuza ya fadi hakan ne a wajen wani shirin da aka watsa kai tsaye na wani gidan rediyon dake jihar Muramvya, mai tazarar kilomita 50 daga gabashin birnin Bujumbura, fadar mulkin kasar Burundi.
A Cikin bayanin sa, kanar Baratuza ya mayar da martani kan zargin da wasu 'yan siyasan kasar suka yi cewar akwai rabuwar kai tsakanin sojojin 'yan kabilar Hutu da 'yan kabilar Tutsi. Inda ya ce zargin ba gaskiya ba ne, kana babu alaka tsakanin lamuran kashe wasu hafsoshi 2 a ranar Talata.
Kamata ya yi, a cewar kakakin, a jira sakamakon binciken dake gudana.(Bello Wang)