Kafin shugaban na Afirka ta kudu ya tashi daga filin jirgin saman Bujumbura, sai da ya fidda wata sanarwa dake kira ga gamayyar kasa da kasa, da su ci gaba da nuna goyon bayan su ga jama'ar kasa ta Burundi, domin kaiwa ga samun damar shimfida zaman lafiya da ci gaba, tare da gina kasar tasu yadda ya kamata.
Babbar tawagar wakilan AU din dai ta kai zayarar aiki a kasar Burundi ne tare da manyan shugabannin ta biyar daga kasashen Afirka daban daban, ciki hada da shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz, da shugaban kasar Gabon Ali Bongo, da na Senegal Macky Sall, da kuma firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn.
Haka kuma, cikin kwanaki biyu da tawagar ta kwashe tana ziyarar aiki a Burundi, wakilan tawagar sun yi shawarwari da gwamnatin kasar, da kuma wasu bangarori da abun ya shafa, inda aka yi alkawarin cewa, za a warware dukkan matsalolin siyasa ta hanyoyin zaman lafiya da fahimtar juna.
Tun daga watan Afirilun shekarar 2015 ya zuwa yanzu, kasar ta Burundi ke fama da tashe-tashen hankula, sakamakon kin amincewar da 'yan adawa suka nuna ga aniyar sake shigar shugaba Pierre Nkurunziza babban zaben shugabancin kasar bisa amincewar jam'iyya mai mulki.
Rikice-rikicen da suka auku a kasar sakamakon wannan sabani, sun sabbaba rasuwar mutane sama da 400, yayin da kuma wasu sama da dubu dari biyu suka tsere zuwa kasashen ketare. (Maryam)