in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman kanun labarun jaridun Najeriya
2016-04-19 18:40:05 cri

A yunkurin kare matsayin sa na shugaban majalissar dattijan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya roki kotun da'ar ma'aikata dake gudanar da shari'ar sa, bisa wasu laifuka 13, da ta dauke masa halartar zaman ta na rana-rana. (Vanguard)

Hukumar EFCC ta cafke Warimopei Dudafa, mataimaki na musamman game da harkokin cikin gida na tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. Ana dai zargin sa ne tare da dogarin tsohon shugaban kasar kanar Ojogbane Adegbe, da laifin rabawa wakilan jam'iyyar PDP wasu kudade da suka kai Naira biliyan 10 cikin watan Disambar shekarar 2014, domin zabar tsohon shugaba Jonathan a matsayin dan takarar jam'iyyar ta PDP, gabanin babban zaben kasar na 2015. (The Punch)(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China