Da isarsa filin jirgin saman kasar a Bujumbura, hedkwatar mulkin kasar, Ban ya samu kyakkyawar karba daga mahukuntan kasar da dandazon al'ummar kasar dake nuna farin cikinsu game da ziyarar tasa.
Daga bisani, ya samu ganawa da shugabannin siyasar kasar, da suka hada da Pascal Nyabenda, shugaban jamiyya mai mulkin kasar, da shugabannin kungiya mai rajin kare demokaradiyya ta kasar CNDD-FDD, da Agathon Rwasa shugaban gamayyar jamiyyar kwatar 'yanci ta FNL da kuma Leonce Ngendakumana, shugaban jam'iyyar dimokuradiyya, Sahwanya-FRODEBU.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar tasu, shugaban jamiyyar (Sahwanya-FRODEBU) ya ce, sun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da yadda za'a magance rikici a kasar ta Burundi, da batun ba da jam'iyyun kasar damar gudanar da al'amurransu, da yadda za'a bude tattaunawar sulhu, da sake bude gidajen radiyoyi na kasar, da ci gaba da aiwatar da ayyukan kungiyoyin fafaren hula, da sakin fursunonin siyasa, da duba yadda za'a sake mayar da 'yan gudun hijira gidajensu. (Ahmad Fagam)