Ban Ki-moon da Pierre Nkurunziza sun gudanar da taron manema labaru na hadin gwiwa a wannan rana a birnin Bujumbura, inda Ban Ki-moon ya yi maraba da alkawarin da Nkurunziza ya yi na yin shawarwari da bangarori daban daban na kasar, tare da yin kira ga bangarorin da su koma ga hanyar shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa. Ban ya bayyana cewa, tilas ne shugabannin kasar Burundi su yi imani da ingiza yunkurin siyasa a kasar don tabbatar da cewa, jama'a sun zauna cikin lumana.
Ban Ki-moon ya ce, za a gudanar da taron kolin jin kai na duniya karo na farko a watan Mayu na bana a birnin Istanbul dake kasar Turkiya, inda za a tattauna rikicin Burundi.
A jawabinsa shugaba Nkurunziza ya yi maraba da ziyarar da Ban Ki-moon ya kawo kasar Burundi, kana ya nuna godiya ga MDD bisa ga goyon baya da ta ke nunawa kasar Burundi. Ya kuma yi fatan MDD za ta nuna goyon baya ga yin shawarwari a tsakanin bangarori daban daban na kasar Burundi tare da taimakawa kasar wajen yaki da ta'addanci. (Zainab)