in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsaron gida ne jigon nasarar Brazil in ji Parreira
2015-04-01 15:59:20 cri
Tsohon kocin kasar Brazil, wanda kuma ya jagoranci kulaf din kasar kaiwa ga nasara a gasar cin kofin duniya na shekarar 1994 Alberto Parreira, ya ce kyakkyawan tsarin tsaron gida da kulaf din Brazil ke da shi a yanzu haka ne ya bashi damar farfadowa, karkashin jagorancin sabon mai horas da yan wasan kasar Koci Dunga.

Brazil dai ta doke Chile a wasan sada zumunta da suka buga ranar Lahadi da ci daya mai ban haushi. Shi ne kuma wasa na 8 a jere da Brazil ta samu nasara a cikin sa a baya bayan nan, karkashin jagorancin Dunga.

Kafin Dunga dai ya karbi ragamar jagorancin kungiyar, Luis Felipe Scolari ne ya kasance kocin ta har zuwa karshen shekarar da ta gabata lokaci da kasar ta rasa damar daukar kofin duniya na wancan lokaci.

A cewar Parreira Dunga ya samu nasarar amfani da salon tsaron baya sosai, lamarin da acewar sa ya nuna Brazil na iya samun nasara ta hanyar kare gida, da kokarin cin kwallaye a lokaci guda.

Sakamakon wannan wasa dai ya biyo bayan nasarar da Brazil ta samu kan kasar Faransa, a wasan su na ranar Juma'ar da ta gabata. Wasan da shi ma Brazil din ta lashe 3 da 1.

Yanzu haka dai Brazil za ta buga wasan ta na gaba da Mexico da Honduras cikin watan Yuni.

Wasannin na gaba za su zamo share fage ga shirin kungiyar na fuskantar gasar "Copa America", wanda za a buga daga 11 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yuli mai zuwa a kasar Chile.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China