in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a manta da gasar cin kofin duniya ta Brazil ba
2015-01-08 15:18:36 cri

A ranar 12 ga watan Yunin bara ne aka bude gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya a kasar Brazil da wakar "We Are One" wadda Pitbull, da Jennifer Lopez da Claudia Leitte suka rera.

A cikin kwanaki 32 da aka shafe ana buga gasar, masu sha'awar kwallon kafa daga kasashen duniya daban daban, sun maida hankali kwarai ga gasar ta kasar Brazil, bisa kokarin da ita kan ta Brazil ta yi na karbar bakuncin gasan da ya yi matukar baiwa kowa sha'awa.

A wancan lokaci na bazara, gasar kwallon kafan ta kasance mai cike da nishadantarwa, wadda kuma ta sha sharhi daga bangarori daban daban.

Wani mai sha'awar kwallon kafa dake birnin Fortalezan kasar Brazil mai suna Carlos, ya gamu da sauran masu sha'awar kwallon kafa daga kasashen duniya daban daban ya yin waccan gasa. Inda ya ce, "Har yanzu ina farin ciki kwarai, ganin yadda masu sha'awar kwallon kafa daga sassan duniya daban daban suka zo nan, na gamu da 'yan Uruguay, 'yan Costa Rica, 'yan Mexico, mun zauna tare, mun tattauna, mun kuma kulla abota, a ganina wannan ita ce ma'anar gasar kwallon kafa."

Babban abinda ya fi jawo hankali a ranar 13 ga watan Yulin shekarar ta 2014 kuwa shi ne, yadda kasar Jamus ta lashe kofin da ci daya mai ban haushi, a wasan karshe da suka kara da kasar Argentina. Kuma wannan shi ne karo na hudu da kasar Jamus ta lashe wannan kofi a tarihi. Jamus ta ci nasara a wasanni 6, ta yi kunnen doke a wasa daya, ta kuma ci kwallaye 18, wanda hakan ya zama matsayi mafi girma tsakanin dukkanin kungiyoyin kasashe 32 da suka shiga gasar.

Game da wannan kyakkyawan sakamako, babban kocin kungiyar Joachim Loew ya bayyana matukar farin cikin sa, ya ce, "Kungiyar kasar Jamus tana da hadin kai kwarai. Mun yi imani cewa, za mu iya cimma nasara a gasar a wancan karo."

A ranar 15 ga watan na Yuli, kungiyar kasar Jamus ta koma gida, inda masu sha'awar kwallon kafa na kasar kimanin dubu 400 suka yi mata maraba, a cibiyar kungiyar dake birnin Berlin. Daya daga cikinsu ya bayyana cewa,"Wannan abu ne mai matukar faranta rai. Mun lashe gasar cin kofin duniya. Ina son kasarmu. Mu zakaru ne na duniya. 'Yan wasan kungiyar kasar mu suna da kwarewa, don haka muka zama kungiya mafi karfi a duniya."

A gasar cin kofin duniyar da ta gabata, an jefa kwallaye 171 a zare cikin wasanni 64, kwallayen da yawansu ya yi daidai da na gasar cin kofin duniya na shekarar 1998 na kasar Faransa, gasar da ta kasance mafi yawan cin kwallaye a tarihi.

Har wa yau Netherlands ta lashe Spainiya da ci 5 da 1, Jamus ta lashe Portugal da ci 4 da nema, kuma Jamus doke Brazil da ci 7 da 1, wadannan wasanni sun kayatar da jama'a matuka. Game da wannan, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Joseph Blatter ya bayyana cewa,"Gasar cin kofin duniyar ta wannan karo gasa ce ta musamman, wadda ta kunshi wasanni masu ban sha'awa ga dukkanin duiya. Wandda ta kunshi wasanni da aka fafata sosai a cikin su, ciki hadda wasan karshe, wanda shi ma ya kayatar matuka."

A kowane karo ya yin gasar cin kofin duniya, akan samu sabbin 'yan wasa da tauraruwar su ke haskawa. Kuma babu shakka a gasar ta Brazil an samu matasa da suka haskaka matuka. Alal misali, dan wasan kasar Colombia James Rodríguez da ke da shekaru 23 da haihuwa, ya ci kwallaye 6 a gasar, tare da lashe lambar yabo ta dan wasa mafi zura kwallaye a gasar ta wannan karo.

Bayan kammala gasar da kwanaki 10 ne kuma kungiyar Real Madrid ta daddale yarjejeniya da shi, bisa kwangilar da ta kai kudin Euro miliyan 80, matsayin da ya kai na hudu a tarihin sayen 'yan wasa mafiya tsada a duniya.

Kana dan wasan Jamus Mario Götze mai shekaru 22 da haihuwa, shi ma ya ci kwallo daya a wasan karshe tsakanin Jamus din da Argentina, kwallon da ta baiwa Jamus din damar lashe Argentina da ci daya da nema, tare da daukar kofin duniya na wannan karo. Kuma ya zamo tauraron kungiyar ta Jamus. Game da hakan ya bayyana cewa,"Ban san yadda hakan ta faru ba. Kungiyar mu ta yi farin ciki matuka, kuma dukkan al'ummar Jamus sun yi murna kwarai, wannan lamari ya zamo tamkar mafarki gare ni. A ganina, na samu babbar sa'a, ina alfahari da kungiyarmu."

Ban da sabbin 'yan wasa da suka nuna bajimta a gasar cin kofin na duniya, akwai kuma tsofaffin 'yan wasa da dama, da suka yi ban kwana da kwallo bayan buga gasar cin kofin na duniya, kamar Xavier daga Spainiya, Andrea Pirlo daga kasar Italiya.

A daya bangaren dan wasan Jamus Miroslav Josef Klose, mai shekaru 36 da haihuwa ya yi suna sosai ya yin gasar ta wannan karo, domin ya ci kwallaye biyu a wannan karo, wanda hakan ya sanya jimillar kwallayen da ya ci, a dukkanin wasannin da ya buga a gasar cin kofin duniya karo hudu suka kai 16, kuma ya kasance dan wasan da ya fi kowanne yawan kwallaye a gasar cin kofin duniya a tarihi.

Yayin da yake zantawa da 'yan jarida game da wannan nasara da ya samu, Klose wanda ke murmushi ya bayyana cewa,"Alal hakika ban yi zaton zan kafa sabon tarihi na bajimta a kwallon kafa ba. Amma ina son in ce kungiyarmu ta nuna kwarewa ya yin wannan gasa, dukkanmu mun yi kokari, mun hada kai da juna, don haka muka samu nasara a wannan karo." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China