A wata sanarwar da hukumar kula da tatttalin arzikin kasashen Afrika ta MDD ta fitar, ta ce, taron na kwanaki 3 ne, kuma an shirya taron ne da nufin tattaunawa game da yadda za'a bunkasa samar da bayanan kididdiga da kuma yadda za'a aiwatar da shirin cigaban karni wato SDGs.
A jawabin da ya gabatar na bude taro, shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome, ya bukaci a bullo da sabbin dabarun tattara bayanai na zamani game da yanayin muhalli domin samun ci gaba a shiyyoyi da ma duniya baki daya.
Ya ce ba za'a iya cimma burin SDGs nan da shekarar 2030 ba, muddin ba'a yi amfani da sabbin dabarun samar da bayanai na zamani game da yanayin kasa ba.
Teshome ya kara da cewar babban abin da ake bukata a Afrika shi ne, samar da kyakkyawan shugabanci, da zaman lafiya, kuma hakan ba za ta samu ba matukar ba'a yi amfani da kyakkyawan tsari a sha'anin kula da filaye ba a nahiyar.
Oliver Chinganya, daraktan cibiyar tattara alkaluman kididdiga ta Afrika ECA, ya bukaci kasashen Afrika da su maida hankali wajen tsara taswirar filaye domin inganta cigaban muhalli a nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)