A cewar sakamako na wannan sabon bincike da cibiyar Afrobarometre ta gudanar a cikin kasashen Afrika 36 tsakanin shekarar 2014 da 2015, tun fiye da karni daya da aka kirkiro wutar lantarki, yawancin 'yan Afrika suna rayuwa cikin duhu ko da yaushe ko jehi jehi.
Bisa matsakaici a cikin kasashe 36, kashi 2 cikin 3 kusan kashi 66 cikin 100 na mutanen Afrika suna rayuwa a yankunan da babu wutar lantarki, an samu kyautatuwa ta kashi 14 cikin 100 tun a shekarar 2005. Amma rahoton na bambanta sosai a nahiyar, da kashi 17 cikin 100 a Burundi da kashi 25 a Burkina Faso zuwa kashi 100 bisa 100 a tsibirin Maurice da Masar, in ji wannan bincike.
Haka kuma, binciken ya nuna, kawai kasashen Afrika 6 bisa 10 kimanin kashi 60 cikin 100 suke ainahi cikin wutar lantarki, wandanda suka fara daga kashi 11% na al'ummar kasar Burundi, da 12% a kasar Malawi , da 14% a Burkina Faso, zuwa dukkan kasa a tsibirin Maurice da kuma Tunisiya.
Amma wani misali na Najeriya shi ne, al'ummar kasar kashi 96 cikin 100 suke da layin wutar lantarki, amma kawai kashi 18 cikin 100 suke samun wutar lantarki yawancin lokaci ko jehi jehi, a cewar wannan bincike. (Maman Ada)