Shugabar cibiyar IITA Katherine Lopez ta ce, bangarorin biyu sun amince da inganta hadin gwiwa wajen kyautata amfanin gona, kamar su doya, da ayaba, da kayan lambu da coco da dai sauransu. Ta kara da cewa, za a iya taimakawa kasashen Afrika wajen habaka aikin gona ta hanyar amfani da shirin mu'amalar dalibai da masu nazari na Sin da Afrika a karkashin inuwar hadin gwiwa.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, nan gaba, hukumomi biyu, za su kara hadin gwiwa da kamfanin aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba na kasashen yammacin Afrika wato GAWAL, don yalwata hadin gwiwa dake tsakanin cibiyar IITA da sauran hukumomin nazarin aikin gona na kasar Sin.(Bako)