Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta ketare muhimmin lokaci tare da shirya, cikin nasara, zabuka cikin 'yanci da adalaci, in ji mista Ladsou, a cikin wata sanarwa ta MDD.
Rantsar da shugaba Touadera da kuma amincewa da sabon kudin tsarin mulki na tabbatar da kawo karshen mulkin wucin gadi da kuma bude wani sabon babi ga wannan kasa, a cewar jami'in na MDD.
Sabuwar gwamnati dole ne ta gudanar da muhimman ayyukan a zo a gani ga dukkan 'yan Afrika ta Tsakiya. Bukatun da aka jira daga wannan gwamnati suna da yawa, wadanda suka hada da zaman lafiya da tsaro masu karko har ma da batun kyautatuwar zaman rayuwar jama'a, in ji mista Ladsou. (Maman Ada)