Rahoton ya bayyana cewa yin amfani da makamashi a kowane gida a kasashen da ke kudu da hamadar Sahara yau da shekaru 15 da suka gabata yana kashi 30 cikin 100 bisa kwatankwacin bangaren kudancin Asiya, idan aka kwanta da na yanzu dake kashi 24 cikin 100.
Tsarin Afrika nada karfin samar da wutar lantarki gigawatt (GW) 90 kuma rabin wannan na kudancin Afrika, yayin da shan wutar lantarkin kasar Spain ya wuce dukkan na kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara.
Baya ga Afrika ta Kudu, shan wutar lantarkin kowane gida a yankin na bisa matsakaici kimanin kilowatt-hours (kWh) 162 a kowace shakara. Wannan na kwatantuwa da matsakaici na duniya na kWh 7.000, in ji rahoton, tare da kara cewa "kasashen da ke kudu da hamadar Sahara na cikin rashin makamashi sosai".
Rahoton ya kara da cewa mutum biyu cikin mutum uku a yankin, wato kimanin mutane miliyan 621 a jimilce, ba su samun wutar lantarki mai inganci.
Gamayyar kasa da kasa ta tsaida burin cimma muradun samun wutar lantarki ta zamani ga duniya nan da shekarar 2030, amma kuma rahoton ya bayyana cewa har yanzu kasashen da ke kudu da hamadar Sahara ba ta bisa hanya mai kyau domin cimma wannan muradin. (Maman Ada)