Rahoton ya ce, sakamakon yanayin El Niño, daga watan Oktoban shekarar 2015 zuwa watan Janairu na shekarar 2016, yawan ruwan sama da aka samu a kudancin kasashen Afrika shi ne mafi kankanta cikin shekaru 35 da suka gabata, yayin da yanayin da ke yankin ya kai matsayin koli a cikin shekaru 10 da suka gabata. A cikin watanni masu zuwa, za a ci gaba da samun ruwan sama kamar yadda ake yanzu, lamarin da ke nuna cewa, yankin zai fuskanci yanayin fari mai muni da ba a taba ganin irinsa ba.
Rahoton ya ce, a kudancin kasashen Afrika kuwa, kimanin mazauna kauyuka sama da miliyan 40 da matalauta kimanin miliyan 9 ne ake kyautata zaton za su dandana radadin matsalar da yanayin El Niño ta haddasa. Rahoton ya ce, an samu matsalar karancin hatsi a kudancin kasashen Afrika na tsawon shekaru 2 a jere, don haka ya kamata kasashen da abun ya shafa su inganta hadin gwiwa, da bullo da tsare-tsaren warware wannan matsala, da daukar matakai tare, don tabbatar da samar da isasshen abinci.(Bako)