in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta cafke mutumin da ya jagoranci harin ofishin MDD dake Abuja
2016-04-11 09:55:15 cri
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cafke Mohammed Usman, wani komandan Boko Haram da ake zargi da kasancewa kusa a harin ranar 26 ga watan Augustan shekarar 2011 kan ofishin MDD dake Abuja, babban birnin Najeriya.

Kakakin ministan tsaron kasa, Tony Opuiyo ya bayyana a cikin sanarwar ta ranar Lahadi cewa wanda ake zargin, da kuma ake kiransa Khalid al-Barnawi, an kama masa ne a Lokoja, dake jihar Kogi, inda ya boye bisa wani sunan jabu. Cafke shi wata babbar nasara ce wajen yaki da ta'addanci, in ji mista Opuiyo. Haka kuma, ya bayyana cewa mutumin ya kasance wani komandan ta'addanci ne da ya samu horo da kuma shirya ayyukan ta'addanci a Najeriya tare da daukar matasan Najeriya masu rauni cikin aikin ta'addanci domin aike da su samun horo a cikin kungiyar Al-Qaida dake yankin Maghreb (AQMI) dake arewacin Afrika ko gabas ta tsakiya.

Mista Opuiyo, ya jaddada cewa Mohammed Usman ya halarci hare haren ta'addanci da dama a kasar, wanda ya hada da harin ofishin MDD dake birnin Abuja, sace wasu ma'aikatan Turai guda biyu a jihar Kebbi a cikin watan Mayun shekarar 2011 da kisa a cikin jihar Sokoto, sace wani injiniyar kasar Jamus a cikin watan Janairun shekarar 2012, da kuma sacewa tare da kisan wasu 'yan kasashen waje bakwai na kamfanin gine gine na Setraco a jihar Bauchi a cikin watan Fabrairun shekarar 2013 da kuma wani harin kan sojojin Najeriya a Okene dake jihar Kogi. Mohammed Usaman za a gabatar da shi gaban kotu bayan an kammala bincike, in ji mista Opuiyo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China