in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta bude layin jirgin sama kai tsaye zuwa kasar Sin
2016-04-15 09:50:58 cri
Gwamnatin kasar Najeriya ta baiwa kamfanin zirga zirgan jiragen sama na Air Peace, wani lasin gudanar da aiki na sufurin jiragen sama kai tsaye tun daga Enugu, dake kudu maso gabashin kasar, zuwa kasar Sin, a cewar hukumomin kasar a ranar Alhamis.

Shugban kamfanin Air Peace Ltd, Allen Onyema, ya bayyana hakan, a yayin dandalin farko na Enugu kan zuba jari, cewar kamfanin zirga zirgar jiragen sama zai fara nan ba da jimawa ba tashin jiragen sama zuwa kasar Sin tun daga filin saukar jiargen saman kasa da kasa na Akanu Ibiam dake Enugu.

Lokaci ya yi ga Najeriya ta zama wata babbar cijiyar hada hadar sufurin sama a shiyyar tsakiya da yammacin Afrika, in ji mista Onyema.

A cewarsa, babu wani kamfanin jiragen sama a yammaci da tsakiyar Afrika dake zuwa kasar Sin kai tsaye. Tare jaddada cewa, za mu kai fasinjojinmu da suka fito daga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika tun daga Enugun Najeriya kana mu tafi da su zuwa kasar Sin.

Mista Onyema ya sanar da cewa kamfanin Air Peace zai tashi kuma zuwa kasashen Indiya, hadaddiyar daular kasashen Larabawa, Afrika ta Kudu, da Atlanta dake kasar Amurka, tare bayyana cewa tashi zuwa kasar Sin zai fara nan da 'yan watanni masu zuwa.

Wannan sabon lasin zai bude wani sabon ga makomar tattalin arzikin jihar, in ji mista Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Enugu, a yayin bikin rufe dandalin farko na Enugu kan zuba jari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China