in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta sake damke jagoran Boko Haram
2016-04-14 20:51:43 cri
Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa ta sake kama wani jagoran mayakan Boko Haram, kwanaki kadan bayan kama Khalid Al-Barnawi, wanda aka jima ana nema ruwa a jallo bisa zarginsa da shirya harin bam a harabar ofishin MDD dake Najeriyar a shekarar 2011.

Bayanai game da binciken farko sun tabbatar da cewa, Bello Danhajia, mukaddashi ne ga jagoran kungiyar Al-Barnawi, kuma ana zarginsa da hannu a laifuka da dama da suka hada da satar shanu da wasu muggan laifuka masu yawa.

Abdulalhai Garba, jami'i ne a hukumar tsaro ta DSS ya shedawa 'yan jaridu a Abuja a jiya laraba cewa, za'a gurfanar dashi a gaban shari'a da zarar an kammala bincike.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China