in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kebe mutane 7 da suka kamu da cutar Lassa a arewa maso yammacin Najeriya
2016-04-15 10:45:51 cri

Darektan hukumar kiwon lafiya ta jihar Katsina ta Najeriya Shamsuddeen Yahaya ya bayyana a jiya Alhamis cewa, an kebe mutane a kalla 7 da suka kamu da cutar Lassa bayan da aka yi bincike kan jininsu a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.

Shamsuddeen Yahaya ya bayyana haka ne ga manema labaru, kana ya ce, mutum daya kawai ya mutu a sakamakon cutar Lassa a wannan jiha. Sauran mutanen da suka kamu da cutar suna samun jinya yadda ya kamata, ya kuma kara da cewa, wani mutumin da ya kamu da cutar ya riga ya samu sauki.

Ban da haka kuma, an aike da jininsu na mutane 18 zuwa birnin Lagos domin gudanar da bincike, wanda kuma sakamakon ya bayyana cewa, dukkansu ba su kamu da cuta ba.

Shamsuddeen Yahaya ya kuma gaya wa manema labaru cewa, an riga an killace cutar Lassa a jihar Katsina, don kada jama'a su nuna damuwa game da cutar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China