in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An farfado da zaman rayuwa a yankunan da suka fuskanci girgizar kasa a jihar Tibet
2015-04-30 15:34:37 cri

Girgizar kasa mai tsanani da ta abku a kasar Nepal ta yi tasiri ga gundumomin Nielamu, da Jilong, da kuma Dingri na jihar Tibet dake nan kasar Sin, inda kawo yanzu mutane 25 suka rasa rayukansu, kana wasu mutane 4 suka bace, a yayin da mutane 383 suka ji raunuka. Bisa kididdiga bala'in ya ritsa da mutane kimanin dubu 300.

A gundumar Zhangmu ta kasar Sin, inda girgizar kasar ta fi tasiri, wadda kuma ke yankin iyakar kasar da Nepal, kuma tsaron tarihinta ya kai shekaru kimanin dubu daya, a halin yanzu ita ce tashar shige da fice mafi girma a jihar Tibet. Amma a sakamakon girgizar kasar, an samu babban sauyi a yanayin karkashin kasar gundumar, inda ake hasashen yiwuwar ci gaba da samun zabtarewar kasa, da gangarowar duwatsu da laka, da kuma sauran bala'u masu tsanani.

Da tsakar ranar jiya Laraba, mutanen gundumar Zhangmu sun yi kaura zuwa wajen yankin bisa taimakon gwamnati da sojoji, domin kare rayukansu.

Ya zuwa safiyar yau Alhamis, mutane kimanin dubu daya daga gundumar ta Zhangmu sun isa gundumar Lazi, mai nisa kilomita 300 daga gidajensu, inda suke kwana cikin tantuna, tare da samun tallafin abinci mai inganci daga mahukunta.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China