in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama'ar Palestinu a harkokin da suke gudanar cikin adalci
2014-10-27 20:45:17 cri
A yau Litinin 27 ga wata, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya gana da manzon musamman na shugaban Palestinu, kana dan kwamitin gudanarwa na kungiyar 'yantar da Palestinu dake ziyara a nan birnin Beijing.

A lokacin ganawar Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta dade tana nuna goyon baya ga jama'ar Palestinu a harkokin da suke gudanar cikin adalci, tare da sa kaimi ga yin shawarwari kan kawo karshen rikici. Don haka Kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su yi kokarin farfado da shawarwari tsakanin Palestinu da Isra'ila cikin lumana ta kowace hanya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China