in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahmoud Abbas ya yi murabus daga kungiyar PLO
2015-08-23 13:43:10 cri
A daren jiya Asabar 22 ga wata, shugaban Palestinu Mahmoud Abbas ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar'yancin Falesdinawa ta PLO. Wannan ya nuna cewa, watakila ne za a gudanar da zaben kwamitin gudanarwa na kungiyar PLO karo na farko bayan shekaru 19 da suka wuce.

A daren jiya, kwamitin gudanarwa na kungiyar PLO ya kira taronsa a birnin Ramallah, inda ban da Mahmoud Abbas, sauran membobin kwamitin gudanarwa 9 su ma suka yi murabus daga mukamansu. An ba da labarin cewa, makasudin wannan murabus shi ne a tilasta wa kwamitin Palestinu da ya kira taro tun da wuri, domin gudanar da zaben kwamitin gudanarwa cikin sauri.

An labarta cewa, shugaban kwamitin Palestinu dake zaune a birnin Amman, hedkwatar Jordan, Salim Zanoun ya riga ya karbi sakwannin murabus.

Bisa dokokin kasar, bayan samun takardun murabus, Salim Zanoun zai kira taron gaggawa na kwamitin kasar Palestinu dake kunshe da membobi 740, domin zaben sabon kwamitin gudanarwa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China