Zhou ya fadi hakan ne a yayin taron kwamitin asasun bada lamini na kasa da kasa wato IMF, inda ya ce IMS ya gaji tarin matsaloli da kalubale masu yawa sakamakon matsalolin da suka shafi matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya.
Shirin ma'aunin tattalin arziki na SDR zai iya taimakawa wajen warware matsalar da ta addabi shirin garambawul na IMS, in ji mista Zhou.
Shi dai asusun ba da lamani na IMF an kirkiro shi ne a shekarar 1969.
Ma'aunin tattalin arziki na SDR a halin yanzu, ana kwatanta shi ne da darajar kudaden kasashe hudu wato dalar Amurka, da kudin Euro da yen na Japan da pound na Ingila. A shekarar da ta gabata ne, bankin bada lamini na IMF ya shigar da kudin RMB na kasar Sin a shirin ma'aunin SDR, kuma zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Oktoban wannan shekarar ta 2016. (Ahamd Fagam)