in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Rasha ya bukaci a samar da daidaito a kasuwar hada hadar kudi
2014-12-18 13:49:41 cri

Firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya gargadi jama'ar kasar da kamfanoni dake kokarin samun riba a kasuwar hada hadar kudin da ba ta da daidaito yanzu, yana mai kiran abin da ke faruwa a kasuwar a matsayin wasa da hankali.

A lokacin da yake jawabi a wani taron gwamnati, ya ce, dole ne a san cewa, sayan kudaden a farashin da suke a yanzu yana nufin sayen shi ba yadda ya kamata ba, yana mai lura cewa, gwamnati tana da wadatattun kudaden kasashen waje da za su ishe ta tafiyar da harkokin tattalin arziki dake gabanta, yana mai kira da a samar da daidaito a kasuwar hada hadar kudaden a kan lokaci.

Medvedev ya jaddada bayanan da tun da farko wasu manyan jami'an gwamnati suka gabatar da cewar, kudin kasar ruble, an ba shi hasashen kasa yadda ya kamata, don haka bai tafi daidai da ainihin yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da tattalin arzikinta ba.

Firaministan ya ce, don haka gwamnati za ta yi aiki ne a wani hadin gwiwwa na kut da kut da babban bankin kasar. Wannan ne taron gwammati karo na biyu cikin kwanaki biyu da aka yi, musamman game da yanayin da ake ciki a bangaren kudin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China