Ma'aikatar shari'a da baitulmalin kasar Amurka sun sanar da cin tarar wasu manyan bankuna shida ciki har da bankin Barclays wadda da ta kai dalar Amurka biliyan 5.8 bisa laifin kayyade yadda kudin musaya zai kasance.
Wadannan bankuna shida su ne bankin Barclays da bankin Royal na Scotland (RBS)da bankin Citigroup da bankin Union na Switzerland da Bankin Amurka da kuma bankin J.P. Morgan, tarar da ta kasance mafi yawa da aka ci irin wadannan manyan bankuna a tarihi. Daga cikinsu bankin Barclays shi aka fi cin tarar.
Ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka ta ba da sanarwa cewa, ma'aikatan da ke kula da harkokin musayar kudi na bankunan 5 sun kayyade yawan kudin musaya na dalar Amurka da kudin Euro ta hanyar tattaunawa a asirce, hakan ya kawo illa ga muradun masu kasuwar musayar kudi, masu zuba jari da hukumomin da abin ya shafa.(Lami)