in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun ajiyar kota-kwana na Amurka zai ci gaba kan manufofinta
2013-08-01 11:56:26 cri
A ranar Laraba, asusun ajiyar kota-kwana na Amurka ya sanar da cewa zai ci gaba kan manufofinsa na bude bakin aljihu domin a bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi.

Harkokin tattalin arzikin kasar sun habbaka a watanni shidan farko na shekarar nan.

A fuskar kwadago kuma akwai kyawawan alamu a 'yan watannin nan to amma har yanzu akwai koma baya a fuskar rashin aikin yi, in ji asusun a bayani da ya bayar bayan ganawa ta kwanaki biyu kan manufofi na kwamitin kasuwanni na asusun (FOMC), wanda shi ne ke nazarin ka'idar kudin ruwa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an samu bunkasa a fuskar kudade da ake kashewa ta harkokin gida da cinikayya, sannan fuskar gidaje ita ma ta kara inganci, to amma farashin gidajen sun haura inda hakan ke kawo cikas ga bunkasar tattalin arziki.

Domin a samu habbaka farfadowar tattalin arziki da kuma tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki bai wuce misali ba, babban bankin kasar ya tsai da shawarar ci gaba da sayen hannayen jari kan dalar Amurka biliyan 40 a kowane wata, da kuma na dala biliyan 45 kowanne wata na tsawon wani lokaci, inda hakan zai kawo inganci ga manufofinta na rage tsawon wa'adin kudin ruwa wanda ake kira QE3. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China