Haka zalika, majalisar dattawan za ta kada kuri'u kan wannan daftari cikin mako mai zuwa. An kuma bayyana cewa daftarin bai shafi harkokin karbar haraji, da inshorar jinya, da aikin ba da kariya ga rayuwar jama'a da dai sauran muhimman fannoni.
Daga bisani shugaba Barack Obama na Amurkan ya ba da wata sanarwa, inda ya yi maraba da matakin da jam'iyyar dimarat da takwararta ta Refubilikan suka dauka na cimma matsaya guda kan wannan daftari.
Sakamakon 'yan bambance-bambancen da ke tsakanin jam'iyyoyi biyu na kasar cikin 'yan shekarun nan, majalisar dokokin kasar Amurkan sun sha fama da matsalolin rashin cimma daidaito, wanda ya sanya gwamnatin kasar kaiwa ga kusan rufe kofar gudanar da ayyukan ta.
Haka nan kasa cimma matsaya guda tsakanin jam'iyyoyin biyu kan wani daftarin kasafin kudi a watan Oktobar da ya gabata, ya tilasa gwamnatin kasar rufe kofarta a karon farko cikin shekaru 17 da suka gabata. (Maryam)