Cigaban da aka samu cikin shirin siyasa musamman ma dalilin dandalin Bangui da tura jojojin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Afrika ta Tsakiya (MINUSCA) zuwa wasu yankunan kasar 40 sun taimaka wajen kyautata matsalar tsaro ko da yake har yanzu akwai sauran aiki, in ji mista Gaye a yayin da yake gabatar da wani rahoto a gaban kwamitin sulhu na MDD.
A cewarsa, wannan kyautatuwa ta taimaka wajen dawowar wadanda suka kaura a cikin gida zuwa muhallinsu da fara gudanar da ayyukan tattalin arziki. Wadannan kai da kawo na koma wa gida na faruwa ne musamman ma a yankunan da aka jibge sojojin MINUSCA.
Amma duk da haka, akwai yankunan kasar da dama dake fama da hare haren kungiyoyin dake dauke da makamai, in ji jami'in. Tawagar MINUSCA ya samu bayanai ko da yaushe na kuntatawa jama'a, fashi da makami, tsare mutane ba bisa doka ba ko munanan ayyukan keta hakkin dan adam.
Manzon musamman na MDD, ya tunatar cewa har yanzu matsalar jin kai a fadin kasar na cikin mawuyacin hali inda mutane fiye da miliyan 2.7 ke bukatar agajin gaggawa, 'yan gudun hijira dubu 450 ke kasashe makwabta kana kuma kusan mutane dubu 400 suka kaura zuwa wasu yankunan kasar. (Maman Ada)