Haq ya fada wa kafofin yada labaru cewa, a cikin sabon zargin da ake yi wa sojojin kiyayen zaman lafiyar M.D.D., har da cin zarafin jama'ar kasar Afrika ta tsakiya, amma Haq bai fayyace abubuwan da hakan ya kunsa ba. Har wa yau wani jami'i na daban ya ce cikin mutanen da aka ci zarafinsu har da yara kanana.
Tuni dai tawagar ta M.D.D. wadda ta tashi zuwa Afrika ta Tsakiya ta bayyana cewa, an samu zargin cin zarafin jama'a har karo 7. Bisa binciken da aka yi, an ce wadannan laifuffuka 7 da ake zargin an aikata, sun faru ne a tsakanin watan Satumba da Disambar bara, kuma sojojin kiyaye zaman lafiya da ake tuhu da aikata su, sun fito ne daga kasashen Kongo(Brazzaville), da Kongo(Kinshasa). Kana M.D.D. ta riga ta bukaci kasashen biyu da su gudanar da bincike.
Bisa tsarin da aka yi, an ce, M.D.D. za ta gudanar da bincike, tare da mayar da wadannan mutanen da ke da hannu cikin lamarin gida, amma ba ta da ikon kaddamar da su gaban kuliya, an ce kasashen su ne kadai ke da ikon gudanar da shari'ar su. (Bako)
A ranar 4 ga watan nan ne, M.D.D. ta ce za a kawar da sojojin kiyaye zaman lafiya na Kongo(Brazawille) su 120.(Bako)