An samu wannan rahoton bincike ne bisa nazarin ayyukan sojojin Faransa sama da su 10, da wasu sojoji 'yan asalin Eqauterial Guinea, da na Chadi, wadanda aka ce sun ci zarafin yara a kasar Afirka ta tsakiya tsakanin watan Disambar shekarar 2013 zuwa watan Yuni na shekarar 2014.
An ce wadannan sojoji basa cikin masu aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D a lokacin. Duk da haka, a cewar rahoton, M.D.D. tana da hakkin gudanar da bincike a kan su, sabo da sun keta hakkin dan Adam.
Sai dai a cewar wannan rahoto, wasu hukumomin M.D.D. wadanda suka nazarci wannan batu, sun yi kunnen uwar shege game da korafe-korafen da aka gabatar.
A cikin rahoton, an ce, tsohon babban jami'in M.D.D. mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar Afrika ta tsakiya Babacar Gaye, da sauran jami'ai 2 na M.D.D. ba su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata ba. (Bako)