Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar suka bayar, an ce, a tashoshin jefa kuri'un da ke birnin Bangui, da sauran yankunan kasar daban daban, masu zabe sun yi layukan kada kuri'u, kuma zaben ya gudana cikin tsarin bin doka da oda.
A cikin dukkanin 'yan takarar shugabancin kasar, dan takarar jam'iyyar farfado da kasa ta kasar wato Anicet Dologuele, da dan takara mai zaman kansa wato FaustinTouadera su ne kan sahun gaba. (Bako)