in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta bukaci Karin hadin gwiwwa da birnin Qingdao na kasar Sin
2016-01-07 10:08:18 cri
Gwamnatin kasar Zimbabwe da birnin Qingdao na kasar Sin a ranar laraban suka rattaba hannu akan yarjejeniyar hadin gwiwwa don tafiyar da ciniki da kasuwanci a tsakanin bangarorin biyu.

Karkashin jagorancin Mataimakin magajin garin Qingdao Wang Wei, mambobi 10 na tawagar kasar Sin da suka hada da wakilan birnin Qingdao akan ayyukan zuba jari na kasashen waje, Bankin Qingdao na kasar Sin, da sauran wadanda aikin ya shafa suka isa kasar ta Zimbabwe a ranar talata domin neman ayyukan da zasu zuba jari a ciki inji kamfanin dillancin labaran kasar New Ziana.

Tawagar dai ta kai wannan ziyarar ne sakamakon irin haka da mataimakin Shugaban kasar ta Zimbabwen ya kai mata a tsakiyar shekarar bara.

Ministan kananan masana'antu , tattalin arziki da inganta zuba jari na kasar Zimbabwen Lazarus Dokora yace yarjejeniyar yana da muhimmanci wajen inganta hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasar sa da birnin na Qingdao.

Yace suna da tabbacin cewa wannan yarjejeniyar hadin gwiwwar zai samar da aiwatar da ayyukan zuba jari masu ma'ana zuwa Zimbabwe daga kasar da ta fi girman tattalin arziki na biyu a duniya wato kasar Sin. A nashi bangaren Mr. Wang Wei ya ce birnin Qingdao ta fi sa idon ta a kan Harare babban birnin kasar da kuma birnin Bulawayo wajen tabbatar da rarraba ayyukan zuban jari yadda ya kamata.

Shi ma a ta bakin shi Kansilan tattalin arziki a ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwen Li Yaohui yace ziyarar wadda tazo sakamakon ziyarar da Shugaban kasar Sin ya kai kasar a watan Disanba na da manufar kara zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China