Mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa wanda ya bayyana hakan a birnin Harare, fadar mulkin kasar yayin bikin kaddamar da gidauniyar neman taimako, ya ce gwamnati na shirin shigo da tan miliyan 1.4 na hatsi a wannan shekara, domin rabawa 'yan kasar kimanin miliyan 3 da matsalar fari ta shafa.
Kasar Zimbabwe wadda ta dogara da harkar noma wajen samun kudaden shiga, yanzu haka tana fama da matsalar farin da ba ta taba ganin irinsa ba yau kusan shekaru 60 da suka gabata sakamakon matsalar sauyin yanayi ta El Nino. (Ibrahim Yaya)