in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben 'yan majalisar dokoki na kasar Syria
2016-04-13 14:38:46 cri

An fara jefa kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki na kasar Syria a yau Laraba, inda 'yan takara fiye da dubu 3 za su nemi kujeru 250 a majalisar.

An fara jefa kuri'u ne da misalin karfe 7 na safe, kuma za a kammala zaben bakin karfe bakwai na yamma. Hukumar zabe ta kasar Syria ta bayyana cewa, an kafa rumfunan zabe fiye da dubu 7 a duk fadin kasar. Idan kuma hukumar ta yarda, za a iya tsawaita lokacin jefa kuri'u har da awoyi biyar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China